Shugaba Muhammadu Buhari ya sake jaddada cewa zai tabbatar wa ‘yan Najeriya da duniya cewa zai tsaya ya tabbatar ya ga an gudanar da za?en 2023 lami lafiya, kuma sahihi, kar?a??e babu magu?i.
A cikin bayanin sa na ?arshen shekarar 2022, Buhari ya ce duk wanda ‘yan Najeriya su ka za?a, shi za a bayyana a matsayin shugaban ?asa, kuma shi zai dam?a wa mulki.
Buhari ya nuna jimami tare da yin ta’aziyyar wa?anda ya ce “mutuwa ta riske su ba su samu damar ganin ?arshen shekarar 2022 ba, kuma ba su samu tsallakawa cikin shekarar 2023 ba.
Ya ce a yanzu da shekara ta zo ?arshe, lokaci ne wanda za a tsaya a yi tambihin baya, a yi nazarin yadda yau ta ke, tare da kirdadon abin da gobe za ta zo mana da shi.
“Wannan shekara ta 2022 ta na da matu?ar muhimmanci a wuri na. Saboda daga yau bai fi saura wata biyar ba na mi?a mulki ga wanda za ku za?a.
“Ina tabbatar ma ku da cewa INEC ta tashi hai?an wajen ganin ta yi za?e ingantacce kuma sahihin da zai zama kar?a??e.”
Da ya koma kan wasu muhimman nasarorin da aka samu, Buhari ya ce ‘yan Boko Haram sama da 82,000 da iyalan su ne su ka tuba daga aikata ta’addanci.
Daga nan ya ci gaba da bayyana nasarorin da gwamnatin sa ta samar a cikin 2023 da ma sauran shekaru fiye da bakwai da ya yi kan mulki, wa?anda a yanzu ya ce nan da watanni biyar zai kammala wa’adin sa na shekaru takwas.