Safarar Muggan Kwayoyi: NDLEA Ta Nesanta Kanta Da Kyari

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa bada?alar kama DCP Abba Kyari kan zargin hannu a safarar hodar Iblis ta ?auki sabon salo a ranar Laraba bayan da hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi NDLEA ta musanta cewa akwai hannun jami’anta a lamarin.

A ranar Litinin ne dai, rundunar ?an sanda yayin da take sanar da kama Abba Kyarin, ta ce asalin mutanen da aka kama da hodar ta Iblis a Enugu, sun shiga ?asar ne da taimakon jami’an hukumar ta NDLEA.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta NDLEA ta fitar ranar Laraba ?auke da sa-hannun kakakinta Femi Babafemi, hukumar ta ce ba ta da wani dalili na ?oye duk wani da bincike ya biyo ta kanta a muna-munar ta hodar Iblis mai nauyin kilogram 25 wadda DCP Abba Kyari ya jagoranta.

NDLEA ta ce ta du?ufa wajen amfani da hujjoji wajen gudanar da bincikenta kuma duk wani mur?e gaskiya ba zai sa ta yi rauni ba.

Babu ko shakka hukumar na mayar da martani ne ga wasu bayanai da ke ?unshe a cikin sanarwar da rundunar ?an sanda ta fitar ranar Litinin tana sanar da kama DCP Kyari da wasu jami’anta hu?u tare da mi?a su ga hukumar.

Sanarwar ?an sandan dai ta yi zargin cewa jami’an ?an sandan sun yi aikin batar da sahun hodar iblis din ce da hadin bakin wasu jami’an hukumar ta NDLEA da ke filin jirgin sama Enugu.

Sanarwar ta kuma ce mutanen biyu da suka zo da hodar Ibilis ?in daga Habasha, sun tabbatar da cewa suna irin wannan hul?a da jami’an hukumar da ke filin jirgin Akanu Ibiam da ke Enugu tun bara; kuma ko a wannan karon da aka kama su, jami’an hukumar ne suka share musu hanya; kasancewar an turo musu hotonsu da sauran bayanansu kafin su sauka a Enugu.

Don haka rundunar ?an sandan ta ?alubanci hukumar da ita ma ta bayyana sunayensu kuma ta ?auki matakin hukunta su.

To sai dai wannan sanarwar da hukumar NDLEA ?in ta fitar ta musanta hannun duk wani jami’inta a cikin wannan badakalar tana mai kafa hujja da zantarwar da DCP Kyari ya yi da jami’inta wanda ya tona shi da kuma bayanan ?aya daga cikin yara Kyarin ASP Bawa James ya bayar cewa wani mai kwarmata bayanai daga cikin masu safarar ?wayoyin ne ya kira su ?an sanda kai tsaye daga Brazil domin sanar da su cewa ana nan tafe da wannan hodar.

Ta ce a bayanin da ya bayar, ASP James Bawa ya ce wani mai suna IK ne ya kira shi daga Brazil ya ?yan?yasa masa cewa wasu mutane biyu za su zo Enugu ta jirgin saman kamfanin Ethiopian Airlines da hodar Iblis da zimmar idan aka kama su a ?wace hodar a sayar a ba shi na shi kaso.

NDLEA ta kara da cewa hakan ya nuna ?arara cewa akwai tawagar ta Abba Kyari na da da??iyar ala?a da gungun masu safarar ?wayoyin da ke Brazil.

Hukumar dai ta ce ta fitar da wannan bayanin ne domin gyara wasu kura-kurai da ke cikin bayanan da aka bayar a baya amma dai ba za ta raga wa duk wanda aka samu da hannu a ciki ba.

Ko dai wane ne ke da laifi dai damuwar ‘yan kasar ita ce wanda za su ba amana tsakanin ?angarorin jami’an tsaron ?asar daban-daban ganin yadda ake ci gaba da banka?o ?a-ta-gari daga cikin su nan da can.

Related posts

Leave a Comment