Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa ?angaren Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi nasara a ?arar da ya shigar yana ?alubalantar nasarar da wata kotun ta bai wa ?angaren tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau a rikicin jam’iyyar APC mai mulkin Jihar Kano.
A zaman da ta yi yau Alhamis a Abuja, Kotun ?aukaka ?ara ta ce hukuncin da Babbar Kotun Abuja ta yi ba daidai ba ne sannan ta tabbatar da cewa shugabannin da ?angaren Ganduje ya za?a su ne halastattu.
Hukuncin kotun na yau ya bai wa ?angaren Ganduje nasara a duka ?angarori ukun da suka ?aukaka ?arar a kan su, kamar yadda Barista Abdullahi Adamu Fagge ?aya daga cikin lauyoyin ?angaren gwamna ya shaidawa BBC.
Tun farko, ?angaren da Shekarau ke jagoranta ya shigar da uwar jam’iyyar ?ara da kwamitin shugabancinta na ?asa da kuma sakatarenta a ?angare ?aya, sannan suka shigar da shugabancin APC na Kano a ?aya ?angaren, da kuma kwamitin da ya shirya za?en shugabancin jam’iyyar a Kano a wani ?angaren daban.
A za?en da aka gudanar mai cike da rarrabuwar kai a watan Nuwamban 2021, ?angaren Shekarau ya za?i Ahmadu Haruna Zago a matsayin shugaban APC na jiha yayin da tsagin Ganduje ya za?i Abdullahi Abbas.
A makon da ya gabata ne tsagin Shekarau ya yi watsi da wani yun?urin sulhu da jam’iyyar ta ?asa ta yi, inda ta na?a Gwamna Ganduje a matsayin jagoran kwamitin sasanta rikicin da suke yi.
Sai dai ya yi wuri a iya bayyana abin da hukuncin ke nufi ga APC a jam’iyyance musamman ganin yadda ake tunkarar babban za?e na 2023.
