Safarar Muggan Kwayoyi: NDLEA Na Neman Abba Kyari Ruwa A Jallo

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa hukumar ya?i da shan miyagun ?wayoyi a Najeriya NDLEA ta ce tana neman ?an sanda DCP Abba Kyari ruwa a jallo kan zargin safarar miyagun ?wayoyi.

Wata sanarwa da NDLEA ta fitar a yau Litinin ta ce bincikensu ya nuna cewa Abba Kyari na da ala?a da wata ?ungiya da ke safarar miyagun ?wayoyi a ?asashen Brazil da Ethiopia zuwa Najeriya.

Ta ?ara da cewa jami’an NDLEA sun gayyaci ?an sandan don ya amsa tambayoyi game da zarge-zarge amma ya ?i zuwa, “abin da ya sa muka yi wannan taron manema labaran kenan”.

“?in amsa kiran hukumarmu da ya yi da ?in ba mu hadin kai wajen bincike shi ne dalilin da ya sa muka yi taron manema labaran nan a yau.”

Idan ba a manta ba, a watan Yulin 2021 ne rundunar ‘yan sanda ta Najeriya ta dakatar da DCP Abba Kyari mai mu?amin kwamishinan ‘yan sanda bisa zargin kar?ar cin hanci daga Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppid – mutumin da ke tsare a Amurka bisa zargin damfarar miliyoyin dala.

NDLEA ta kamen da aka yi da yawan mutanen da aka tsare a cikin wata 12 da suka gabata alama ce da ke nuna cewa a baya an raina girman matsalar tu’ammali da miyagun ?wayoyi da ?asar ke ciki, kafin Shugaba Buhari ya ?arfafa hukumar NDLEA.

Amma ta ce a cikin wata 12 mafi yawan ?an Najeriya sun yarda cewa ?asar na cikin wata masifa ta tu’ammali da miyagun ?wayoyi kuma suna yaba wa ayyukan NDLEA don da?ile hakan.

Sanarwar ta ce sai dai abin takaicin shi ne yadda wasu jami’an tsaron da ya kamata su ha?a hannu da NDLEA wajen da?ile wannan annoba su ne a gaba-gaba wajen karya dokar, ta wajen ha?a kai da su ana safarar miyagun ?wayoyi a ?asar.

Bayanan sirrin da muka samu sun sa hukumarmu ta yarda ?ari bisa ?ari cewa DCP Kyari ?aya ne daga cikin masu safarar miyagun ?wayoyi tsakanin Brazil da Ethiopia da Nigeria, kuma yana bu?atar amsa tambayoyin da suka bijiro a kan wani batun safarar ?wayoyi da yake jagoranta.

Related posts

Leave a Comment