Rikicin APC: Kwamitin Riko Na Cikin Tsaka Mai Wuya

Shugabancin riko na jam’iyyar APC ?ar?ashin jagorancin Mai Mala Buni na cikin tsaka mai wuya biyo bayan kiran da wasu manya na jam’iyyar suka yi akan a sallami shugabannin jam’iyyar na wasu jihohi.

Shugaban rikon kwaryar Mai Mala Buni na cikin wani yanayi akan kiran da ?usoshin jam’iyyar suka yi, musamman akan batun tun?u?e shugabannin jam’iyyar na Jihohin Kaduna,Legas da jihar Ribas da Ogun.

Majiyarmu ta “The Nation” ta ruwaito cewar manyan ‘ya’yan jam’iyyar wadanda suka ha?a da Gwamnoni da Ministoci ‘yan Majalisun tarayya duk sun shiga cikin batun inda suke neman Kwamitin ri?on da ya tsoma baki wajen shawo kan rikicin.

Tun bayan kama ragamar shugabancin kwamitin rikon ya kar?i ?orafe ?orafe da dama daga wajen ‘ya’yan jam’iyyar wadanda aka musgunamawa.

Wani al’amari ne mai matukar tasiri ga kwamitin rikon jam’iyyar na ganin sun daidaita al’amurra da ?inke dukkanin ?arakar data faru cikin jam’iyyar da daidaita komai cikin watanni shida.

Sai gashi tun kafin aje ko’ina Kwamitin na fuskantar matsin lamba daga wasu ?usoshin jam’iyyar na cewar ya sanya baki cikin rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyar a wasu jihohi.

A takaice wadannan ?usoshin jam’iyyar na neman a rusa shugabannin jam’iyyar na wasu jihohi ne da sake nada sabbi.

A yayin da wasu tuni suka shigar da ?ararraki a gaban Shari’a suna ?alubalantar sahihancin shugabannin jam’iyyar a wasu jihohin.

Da yawa yawansu ?orafe ?orafen nasu na gaban Kwamitin sulhu na jam’iyyar ?ar?ashin Chief Bisi Akande, amma suna cikin gajin ha?urin jiran kwamitin sulhun ya yi aikin nashi suka ?aga batun zuwa Kwamitin ri?on ?warya na jam’iyyar.

Sai dai kamar yadda rahotanni ke nunawa shugaban kwamitin rikon na bakin ?o?arin shi wajen shawo kan matsalolin jam’iyyar, tun a kwanan nan Buni ya gargadi wani minista da cewar ya girmama umarnin shugaban kasa na daidata Jam’iyyar, inda ya bukace shi da yayi kira ga wasu magoya bayan shi sun janye ?arar da suka shigar a kotu.

Hakazalika kwamitin ya shaidawa wani tsohon gwamna kuma Tsohon Sanata cewar kwamitin ba zai saurari komai daga garesu ba har sai idan sun kirayi magoya bayansu da janye ?ararrakin da suka shigar a gaban Kotu suna ?alubalantar shugabancin wasu jihohin.

Kwamitin na iyaka bakin ?o?ari wajen dinke ?arakar da jam’iyyar ke fama da ita a wasu jihohi domin ganin komai ya daidaita kamar yadda shugaban kasa ya bukata.

Babbar matsalar da Mai Mala Buni ke fuskanta a yanzu ita ce rikicin jihar Ribas inda Ministan Sufuri Rotimi Amaechi da Sanata Magnus ke takun sa?a akan wanda ke da alhakin jan ragamar jam’iyyar a jihar.

Related posts

Leave a Comment