Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya ce saboda rashin jajircewar shugaban kasa ko kuma kunyarsa ta yi yawa akan na kasa da shi ne ya sa ya kasa kawo karshen matsalar rashin tsaro dake addabar ?asar.
Sani ya yi wannan maganar ne a ranar Asabar yayin da Daily Trust ta Twitter ta gayyace shi a matsayin bako mai jawabi inda ya yi magana akan rashin tsaro da kuma zaben 2023.
“Mutanen da ke kan madafun iko su na ta gazawa kuma za su ci gaba da gazawa saboda shugaban kasar mu ba ya da karfin daukar mataki akan na kasa da shi.
“Idan ka jagoranci jami’an tsaro, sojoji, ko kuma karamar hukuma ko jiha, kuma ana ci gaba da kai hare-hare yankinka, to ba ka da amfani kuma aikin shugaban kasa ne korar irin wannan, ya maye gurbinsa da wani daban.
“Wani lokaci matsalolin tsaro su na bukatar irin haka. Akwai zargin cewa har da jami’an tsaro ake hada kai ana rura wutar rashin tsaro wanda wannan babban lamari ne da bai kamata a kyale shi ba.”
Ya ci gaba da cewa bai dace mutum ya zura ido yana ganin wanda ya dauka aiki yana zaune ba ya tabuka abin kirki ba. Ya koka akan yadda gwamnati ta kara wa Shugaban Hukumar Gidajen Gyaran Halin Najeriya, shugabannin tsaro da sauransu wa’adi.
A cewarsa babu wata nasarar da aka samu bayan aiwatar da hakan kuma ya kamata shugaban kasa ya kara dagewa wurin yin aikinsa.
