Rashin Ubangida Na Kawo Mana Cikas – Jaruma Suwaiba Abubakar


Tsohuwar jaruma a masana’antar fina-finai ta Kannywood, ta ce, rashin tsayayyen Ubangida yana zama matsala ga jarumai, da dama a wajen samun ci gaba a cikin harkar fim, duk da kuwa suna da Kwarewa.

Jarumar ta bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar su da wakilin jaridar Dimukaradiyya in da ta ke cewa “na shafe tsawon shekaru a wannan masana’antar Amma da ya ke ba ni da tsayayyen Ubangida, har yanzu ba kowa ne ya sanni ba saboda rashin Ubangida, don ka san ita harkar fim duk yadda ka kai ga iyawa to ba za ka samu shiga ba sai kana da daurin gindi, to shi ya sa za ka ga wasu jaruman sun dade ba a san su ba. ”

Ta ce gaba da cewar” a yanzu na shafe tsawon shekaru a cikin wannan masana’antar, amma dai har yanzu babu wani fim da na yi da zan ce na yi fice a duniya, don ka ga akwai wadanda su ka zo a baya na da yawa Amma saboda suna da daurin gindi duniya ta san da su.

Duk da dai na san komai na Allah ne amma dai akwai sila wadda mutum ya ke samu da zai samu ya kai ga nasara, to ita harkar fim sai kana da gata, idan ba haka ba sai dai ka zama dan kallo a cikin harkar, kuma wannan ita ce matsalar da irin mu su ke fama da ita. ”

Daga karshe Jarumar ta yi kira ga masu gudanar da harkar fim din da su rinka duba Kwarewa wajen Daukar jaruman da za su rinka sakawa a cikin fim, ba Wai kawai sanayya ba.”

Related posts

Leave a Comment