Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Bauchi na bayyana cewar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III, ya yi kira ga ‘yan kasuwa suji tsoron ranar ha?uwarsu da Allah kada su kara farashin kayayyakin masarufi yayin da watan azumin Ramadana ke gabatowa.
Sarkin ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar a taron rufe gasar musabaqar Alqur’ani ta kasa da akayi a jihar Bauchi.
“Ramadan na zuwa kuma tsadar rayuwa na kara karuwa. Ina son amfani da wannan dama don kira ga ‘yan kasuwa suji tsoron abinda Allah zai yi musu ranar gobe qiyama idan suka hadu da shi alhali suna masu cutar da bayinsa.”
“Maimakon kara farashin kayan masarufi ku taimaka ku rage farashin don samun albarkar Allah.” “Farashin kayan abinci ya tashi kuma yana cigaba da tashi, wajibi ne gwamnatoci su magance wannan matsalar.”
