Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Filin Jirgin Sama

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar hankulan mutane ya tashi matuka a yayin da gungun wasu ‘yan bindiga suka kai hari filin tashin jiragen sama suka hana jirgi tashi daga filin.

Bincike ya nuna cewa jirgin yana shirin tashi ne zuwa Legas a ranar Asabar, a lokacin da ‘yan Bindigar suka farmaki tashar jirgin hakan yasa ma’aikatan jirgin da fasinjoji suka tsere.

A cewar wata majiya da ta nemi a boye sunanta, ‘yan bindigan sun harbi wani ma’aikacin hukumar kula da sararrin samaniyar Najeriya, NAMA a yayin harin.

Duk da cewa babu cikakken bayani game da harbin ma’aikacin, an gano cewa ‘yan bindigan sun harbe shi ne a titin tashin jirgin.

Rahotanni sun bayyana cewa jirgin da aka shirya ya tashi misalin karfe 12.30 na ranar Asabar ya fasa tashin saboda harin yan bindigan.

Related posts

Leave a Comment