Rage Radadi: Tallafin Dubu Dari-Dari Ba Zai Wadaci ‘Yan Najeriya Ba – Ramalan

An bayyana cewa ko ka?an tallafin rage radadin tsadar rayuwa na Naira dubu takwas-takwas da gwamnatin Tinubu ke aniyar aiwatarwa sakamakon janye tallafin mai ba zai wadaci jama’ar Najeriya ba ko da Naira dubu ?ari ?ari ta raba.

Shugaban Kamfanin ATTAR Communications mamallakan gidajen talabijin da rediyo na Liberty Alhaji Ahmed Tijjani Ramalan ya bayyana hakan a yayin wata tattaunawa da ya yi da wakilinmu a birnin tarayya Abuja.

Ramalan wanda tsohon shugaban tuntuba ne na jam’iyyar APC a Jihar Kaduna ya shawarci shugaban kasa Tinubu da cewar maimakon haka kamata ya yi ya mayar da hankali wajen da?ile satar da sauran ayyukan dake gurgunta cigaban Najeriya domin tsamar da ‘yan kasar daga halin kunci da suke ciki.

“Lokaci ya yi da ya kamata a zauna a lalubo hanyoyin da za su kai Najeriya gaba ta hanyar bunkasa tattalin arzikin kasa da kuma Inganta ci maka ta abinci da samar da tsaro”.

Ya ?ara da cewar kayayyakin tallafin da aka raba a gwamnatin da ta gabata bai ?ara wa ‘yan Najeriya komai ba sai ?arin talauci saboda haka wannan shirin ma da ake ?o?arin yi babu wani alfanu da zai bayar.

Ahmad Tijjani Ramalan ya ?ara da cewar a halin da ake ciki yanzu idan gwamnatin Tinubu ta raba wa’yan Najeriya naira dubu ?ari ?ari ba zai kashe musu ?ishirwar talaucin da suke ciki ba na tsadar rayuwa.

Ya shawarci gwamnatin tarayya ta mayar da hankali wajen inganta harkar samar da abinci ga ‘yan ?asa,ilimi da kiwon lafiya da samar da ingantaccen tsaro a kasa gaba daya.

Related posts

Leave a Comment