Tsohon gwamnan Legas, kuma jagoran jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, ya ce ya fa?a wa shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ?asar a za?en 2023.
Ya bayyana hakan ne bayan wata ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja a ranar Litinin.
A cewar Tinubu “na fa?a wa Shugaba Buhari aniyata, ban ji abun da ba shi na yi tsammanin ji daga gare shi ba, ya ?arfafa min guiwa kamar yadda dumokura?iyya ta ba ni dama, amma har yanzu ban sanar da jama’ar Najeriya ba tukunna, ina ci gaba da tuntu?a.”
“Na shafe tsawon rayuwata ina fatan zama shugaban ?asa, don haka me ya sa zan yi tsammanin jin abun da ya sa?a da wannan daga wajen shi, tsari muke yi da dimokura?iyya, don haka dole mu tafi a kan haka”, in ji shi.
Tun a bara ne hotunan takarar Tinubu suka fara kara?e wasu jihohin Najeriya, ko da yake ya ja bakinsa ya yi gum, in ban da a yanzu da ya sanar da shugaba Buhari wannan fata baki da baki.
Masu lura da lamuran siyasa suna gani Tinubu zai fuskanci ?alubale wajen samun tikitin yi wa APC takarar shugaban ?asa a 2023, musamman ganin yadda shekarunsa suka ja kuma ‘yan kasar na fatan ganin an zabi mai jini a jika. Sai dai wasu ?a?an jam’iyyar na ganin ya kamata a saka masa da wannan takara ko don irin wahalar da ya yi wa APC da shugaba Muhammadu Buhari a za?ukan 2015-2019.
Ko da yake Tinubu ne mutum na farko da ya furta cewa zai yi takara zuwa yanzu, akwai wasu fjiga-jigai a jam’iyyar wa?anda su ma ake kyautata zaton za su yi takara, ciki har da mataimakin shugaban ?asa Farfesa Yemi Osinbajo wanda tuni wasu ?ungiyoyi suka fara yi masa kamfe.
Haka kuma akwai gwamnonin da ake ganin za su fito takarar shugaban kasar.
Akwai kyakkyawan zaton cewa APC za ta mi?a wa yankin kudu maso yamamcin Najeriya takarar shugaban ?asa a 2023, don haka ake ganin cewa Tinubu wanda uban gidan Osibanjo ne a siyasance, a wannan karon zai ?arje gumi da yaronsa na siyasa wato Osinbajo wa?anda dukkansu daga yankin suka fito.
Wasu mutane dai na ?ishin-?ishin ?in cewa ba lallai ne wasu gwamnonin jam’iyyar ta APC musamman a arewacin ?asar su goyi bayan Tinubu ba, yayin da wasu na ganin cewa ya yi kafuwar da ture shi a jam’iyyar sai an shirya.
