Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta karrama Shugaban ?asa Muhammadu Buhari da lambar yabo gabanin taron ?ungiyar Tarayyar Afirka da zai gudana a yau Juma’a.
Jim ka?an bayan isarsa kasar ta Nijar, Shugaba Mohamed Bazoum ya karrama shi yayin wasu bukukuwa biyu da aka yi a ranar Alhamis.
Bayan ba shi lambar yabon, an saka wa wani titi a Yamai sunansa, sannan kuma aka ?addamar da wani littafi da aka fassara daga turancin Ingilishi zuwa na Faransanci game da mulkin Shugaba Buhari.
“Ina fatan wanna littafi zai zama al?ibla ga shugabannin Afirka masu zuwa kuma ya shata musu hanyar jajircewa da nagarta da kuma kishin ?asa.
Shugabanin ?asa da na gwamnatocin Afrika da dama ne suka suka isa Yamai babban birnin ?asar don halartar taron na ?ungiyar African Union.
