Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana gaskiyar sana’ar da yake yi kuma har ya tara dukiya mai yawa. Tinubu ya yi nuni da cewa, duk wani wayayyen dan Najeriyan da sanya kudinsa N1.8m kacal ya zuwa hannun jari a kamfanin Apple a 1980 to ya zuwa yanzu ya mallaki sama da Naira Tiriliyan 10.
A wani rubutu da ya yi ta kafar sada zumunta ta Facebook Tinubu ya bayyana cewa ya mallaki miliyoyin daloli akalla shekaru 10 kafin ya zama gwamnan jihar Legas.
Tinubu ya bayyana cewa, shi mai arziki ne tun lokacin da yake rike da mukamin shugaban NADECO. “Don Allah ku fada ma matasa gaskiya. Ni Asiwaju Tinubu na mallaki miliyoyin daloli tun ina shugaban NADECO akalla shekaru 10 kafin na zama gwamnan jihar Legas.
Ya kamata wasu ma su fito su bayyana silar mallakar biliyoyinsu.” Ya kuma bayyana cewa, shi ba barawo bane, domin a can baya da mutane ke sayen manyan motoci na miliyoyi suna hawa, shi ya yi dabarar zuba hannun jarinsa a kamfanin da zai samar masa da kudi a gaba.
A cewar Tinubu, ire-irensa da suka sa jari a kamfanonin na’ura, a kowace rana suna iya samun dala 1000 ko fi daga hannun jarin.
