NEJA: ‘Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari A Babban Masallaci

Rahotannin dake shigo mana daga Minna babban birnin Jihar Neja na bayyana cewar wasu gungun Yan bindiga dauke da muggan makamai sun kashe mutane biyu sannan sun sace wasu da dama a wani hari da suka kai wani masallaci a ?aramar Hukumar Rafi a Jihar.

Rahotannin sun bayyana cewar ‘yan Bindigar sun kai hari a wata Motar Fasinja inda suka sace Mutane Wadanda aka sace din suna tafiya ne cikin babbar mota suna hanyarsu na dawowa daga kasuwar Juma’a a karamar hukumar Rafi ta jihar.

Rahotannin sun bayyana cewar yan bindigan sun cinna wa babban motar wuta bayan sace fasinjojin da suka yi.

Wadanda aka sace sun hada da: maza, mata da yara. Ba a san inda aka kai wadanda aka sace din ba a lokacin hada wannan rahoton. Lamarin ya faru ne a Tashar Amale a karamar hukumar Rafi na jihar Niger.

Bayan kisa da kuma sace fasinjojin, yan bindigan sun kuma kutsa wani masallaci sun tarwatsa sallar Juma’a da ake yi. Wasu daga cikin masallatan sun yi rauni sakamakon harsashin bindiga. An kuma ce yan bindigan sun kai hari a wasu garuruwa da unguwanni da ke yankin inda suka rika harbin duk wanda suka hadu da shi, yan kauyen sun rika tsere wa amma sun kashe biyu.

Sakataren gwamnatin jihar Alhaji Ahmed Ibrahim Matane ya tabbatar da afkuwar lamarin amma ya ce ba a riga an tabbatar da adadin wadanda yan bindigan suka sace ba. SSG din ya ce: “Tabbas an kai hari kuma an sace fasinjoji amma ba mu riga mu tantance adadin wadanda aka kashe ba da wadanda aka sace.”

Related posts

Leave a Comment