Rahotanni daga Mina babban birnin Jihar Neja na bayyana cewar Jami’an tsaro na Jihar sun samu nasarar halaka ‘yan bindiga da dama da suka dade suna addabar wasu garuruwan da ke karkashin karamar hukumar Munya da Shiroro da ke jihar.
Ayyukan jami’an tsaron sun janyo an samu nasarar kwace dabbobi 500 a garin Kuchi, Galadiman-Kogo, Allawa da garin Erena da ke karkashin karamar hukumar Munya da Shiroro dake jihar ta Neja.
An kwashe dabbobin sannan aka garzaya da su Minna, babban birnin jihar da taimakon mafarauta. Shanu biyar sun mutu kafin a isa dasu Minna saboda matsewar abin hawan da aka zuba su ciki da kuma nisa.
Kwamishinan harkokin kananan hukumomi da harkokin cikin gida na jihar, Emmanuel Umar ya shaida yadda aka samu nasarar kwaso dabbobin wadanda ciki akwai shanu 300 da tumaki fiye da 100.
Za a ajiye dabbobin karkashin kulawar Ma’aikatar Dabbobi ta Jihar. A cewarsa, yayin da aka halaka ‘yan bindiga da dama, wasu jami’an tsaro sun rasa rayukansu amma bai sanar da yawansu ba.
Ya ce yanzu haka ana ta kokarin ganin yadda za a tallafa wa iyalan jami’an tsaron da aka halaka. Kwamishinan ya kula da yadda gwamnatin jihar ta gama shirya hanyoyin da zata gano asalin masu dabbobin don a basu ko kuma su shiga cikin dukiyar jihar.
An samar wa rundunar ‘yan sandan sabbin kayan yaki da motoci don su tallafa wurin yakar ta’addanci a jihar Umar ya kula da yadda rashin tsaro a jihar zai gyaru matsawar aka kawo karshen ‘yan bindiga, masu satar dabbobi, masu garkuwa da mutane da sauransu.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun ya tabbatar da cewa an samar da kayan yaki har da ababen hawa biyar tare da motocin yaki daga hedkwatar ‘yan sanda. A cewarsa ana fatan sabbin kayan yakin za su taimaka wa rundunar wurin kawo karshen ta’addanci a jihar.
