A ranar Alhamis ne mai girma Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana manyan dalilan da yasa bai zai sake tsayawa takara karo na uku ba, wato yin tazarce.
Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya yi magana ne a taron kungiyar kasashe renon Ingila da ya gudana a ?asar Ruwanda.
An gudanar da taron ne a cigaba da taron Shugabannin kasashen renon ingila wato Commonwealth karo na 26 a birnin Kigali na kasar Ruwanda.
Mai girma Shugaban ?asa ya nanata kudurinsa na mutunta iyakar wa’adin mulkinsa bisa kundin tsarin mulkin Najeriya, wanda ya bada damar yin wa’adi sau biyu.
Rahotanni sun bayyana cewar Firaministan ?asar Birtaniya Boris Johnson ne ya tambayi ko Shugaba Buhari zai sake tsayawa takara.
Sai Buhari ya bada amsa da cewa “Wani lokaci kuma? A’a! Mutum na farko da ya gwada hakan bai kare lafiya ba,” in ji shi.
Dangane da rashin tsaro kuwa, Buhari ya ce gwamnatinsa na yin iyaka bakin kokarinta wajen karya ?arfin ‘yan ta’adda, kuma an samu gagarumar nasara.
