Jami’an tsaro na hadin gwiwa tsakanin sojoji, ‘yan sanda, Jami’an kare jama’a da Kungiyar sa kai za su shiga sako da lungun dazuzzuka don ceto yaran makarantar Islamiyya ta Tegina da aka sace.
Gwamnan Abubakar Sani Bello ne ya bayyana haka a yayin da ya ziyarci rundunar don kara masu karfin gwiwa a Kagara hedikwatar karamar hukumar Rafi.
Gwamnan ya ce lokaci ya yi da gwamnatinsa za ta dauki tsantsauran matakai don ganin an kawo karshen ta’adin ‘yan ta’adan wadanda suka chanza yanayin rayuwar jama’a tumma na kauyuka.
“Dole mu yi iya kokarinmu mu ga ba su yi nasarar chanza mana rayuwar mu ba, dama sun fara ne ta korar manoma daga gonakinsu, sai kona masu runbunan hatsinsu sannan suka fara sace mutane wanda alatilas suka sa muka rufe makarantu inda Allah kadai ya dan menene matakinsu na gaba.”
Ya ce duk wasu kayayyakin aiki an samo masu kuma za a rinka biyansu alawus da albashinsu a kai, a kai.
Gwamnan wanda ya yaba wa Jami’an tsaro don namijin kokarin da su ke yi wajen ba da tsaro, ya nuna alhininsa na kashe Jami’an tsaro na sa kai har su 20 a Karamar Hukumar Magana.
Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da kara matse damtsen wajen hadin kai da kasheshen da Nijeriya ke makwabtaka da su don samo mafita a kan tsaron don alamu sun nuna ‘yan ta’adan da suke barna ba ‘yan Nijeriya ba ne.
Tunda farko, gwamnan ya gana da iyayen yaran da aka sace a Fadar Mai Martaba Sarkin Kagara, Alhaji Ahmed Gunna inda ya ba su magana akan su cigaba da hakuri, Gwamnati na iya kokarin gano hanyoyi da yaransu za su dawo gida cikin koshin lafiya.
A wata takarda da Babban Sakataren watsa labarai na gwamna Mary Noel-Berje ta sanya wa hannu ta ce, Sarkin Kagara, ya godewa Gwamna don tallafa masu tumma a fannin tsaro ga masaurautar da kuma taimakawa iyayen yaran da abun ya shafa.
A nashi bangaren Shugaban makarantar Salihu Tanko Islamiyya, Malam Abubakar Alhassan ya ce suna maraba da matakin da gwamnati ta dauka na dumfarar ‘yan ta’adan in da za a kwato masu yara cikin koshin lafiya.
Malam Alhassan ya bayyana cewa yanzun dai malamai 15 na makaranta sun gudo daga hannun masu garkuwa da su a Jihar Zamfara inda yanzun haka suna hannun sojoji a Birnin Gwari na ke Jihar Kaduna inda a ke sa ran za a mika su ga gwamnatin Jihar Nija nan ba dadewa ba.
