Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Hukumar yan sandan farar hula, DSS, ta saki mawakin Tijjaniya Ahmad Abdul, da aka kama saboda fitar da wata waka mai dauke da batanci ga Annabi Muhammad (SAW).
An kama Abdul ne bayan fitar da wata waka mai taken ‘Barhama Gwaska’ da ake yi wa kallon ya yi batanci ciki kuma wakar na iya tada rikici a jihar ta Kano.
Da ya ke tabbatar da sakin a ranar Litinin, Sakataren hukumar tantance fina-finai da bidiyo na jihar Kano, Ismaila Na’aAbba Afakallah ya ce ya samu korafe-korafe da dama game da wakar daga mutane.
Afakallah ya ce ya sanar da DSS game da korafin hakan yasa suka kama mawaki a wani otel da ya boye domin tsoron kada mutanen gari su kai masa hari.
Ya kara da cewa an sada mawakin da yan uwansa bayan shafe kwanaki a hannun DSS. “An sake shi, ya ce ya yi nadamar fitar da wakar kuma ya nemi afuwa, ya yi alkawarin ba zai sake maimaitawa ba,” in ji Afakallah.
Dalilin da yasa ba a gurfanar da shi a gaban kotu ba A kan dalilin da yasa hukumar ta ce bata gurfanar da shi a kotu ba, Afakallah ya ce, “Ba gurfanar da mutane a kotu bane ke gaban mu, burin mu shine su tuba su gyara halayensu.
Ya yi nadama abin da ya yi kuma ya nemi afuwa game da laifin da ya aikata.”
