Neja: Gwamna Ya Harbu Da CORONA

Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello ya kamu da cutar sar?ewar numfashi wadda aka fi sani da CORONA kamar yadda ya sanar da hakan da kansa a wani gajeren sako da ya wallafa a shafinsa na Tiwita.

“Sakamakon Gwajin da akayi min ya nuna na kamu da cutar Korona, duk da ba wata alama da ta bayyana a fili, amma tuni na killace kaina” a cewarsa.

In zaku iya tunawa, hukumar kare ya?uwar cututtuka (NCDC) ta yi garga?in sake ?ullar cutar a karo na biyu, inda ta sanar da ,adadin da ya kai mutum 300 a matsayin sabbin wa?anda suka kamu da cutar a ranar Lahadi.

Tuni dai mutane suka fara shiga firgici da razanin sake ?ullar cutar a karo na biyu, wanda hakan ke nufin cewa za a kara daukan matakan dakile yaduwarta a tsakanin jama’a, kamar yadda aka yi a karo na farko, ta hanyar kulle da shiga matsin rayuwa.

Bayan bullar cutar korona a farkon shekarar 2020, kasashe sun dauki matakan dakile yaduwar korona ta hanyar saka doka kulle tare da bawa jama’a shawarar su nesanta da juna tare da yawaita wanke hannaye.

Dokar kulle ta saka kunci a zukatan jama’a saboda hana kasuwanni, kasuwanni, masana’antu da zirga-zirgar jama’a a manyan tituna da cikin lunguna, da gudanar da ibada a masallatai da coci-coci.

Related posts

Leave a Comment