Hukumar da ke Yaki da Cin Hanshi Hanci da Rashawa EFCC, ta kaddamar da wata manhaja da za ta ba ‘yan kasar damar daukar hotunan abubuwa ko wuraren da ake aikata laifuka kuma su watsa su kai tsaye.
Shugaban hukumar, Abdulrasheed Bawa, wanda ya kaddamar da manhajar Eagle Eye a Abuja ranar Laraba, ya bayyana wa manema labarai yadda ake sauko da ita daga manyan rumbunan manhajoji na wayar salula.
Da yake magana da manema labarai jim ka?an bayan taron, Abdulrasheed Bawa ya ce yun?urin nasu yana cikin shirin nan na kwarmata bayanai da ake kira Whistle Blower a Ingilishi.
“Duk wanda yake so ya kwarmata mata bayanai don ya samu wani abu zai iya yin hakan a ciki kuma ya bayyana cewa ya yi hakan ne a matsayinsa na mai kwarmata bayanai,” a cewarsa.
Ya ?ara da cewa mutum zai iya ?aukar hoton gidan da ake aikata laifin rashawa da kuma adireshinsa ya turo musu, “mu kuma sai mu bincika”.
Abdulrasheed Bawa, mai shekara 40 wanda ya zama shugaban hukumar a watan Fabarairun 2021, ya ce ana iya samun manhajar a App Store ga masu wayoyin Apple da kuma Google Play Store ga masu amfani da Android.
Ya ce: “Wannan manhaja tamu sunanta Eagle Eye. Za ku ga tambarinmu na EFCC kamar yadda aka san shi. Idan aka duba App Store ko Google Play Store za a gan ta da suna Eagle Eye kuma za a ga EFCC a jiki.
“Idan aka sauke ta za ta yi aiki ne kamar yadda Facebook ko WhatsApp yake a waya. Duk lokacin da kake son yin amfani da ita za ka bu?e ne kawai ka fara.
“Mutum zai iya ?aukar hoton gidan [da ake aikata laifin rashawa] da kuma adireshinsa ya turo mana mu kuma sai mu bincika. Idan ya ga dama ya fa?a mana sunansa, idan bai ga dama ba kuma shikenan.”
Sai dai shugaban ya garga?i masu kwarmata bayanai cewa dole ne su tabbata cewa bayanan da za su bayar na gaskiya ne.
“Idan mutum ya fa?a mana bayanai za mu gayyace shi ya zo ya cike wasu takardu sannan kafin a fara za mu fa?a masa cewa idan muka gano bayanan nasa ?arya ne, yana yi ne don tozarta wani, to shi ma fa hannun doka zai kama shi,” in ji shi.
