Majalisa Ta Haramta Biyan Kudin Fansa Ga ‘Yan Bindiga

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Majalisar dattawa ta yi wa dokar ta’addanci ta 2013 gyaran fuska domin haramta biyan masu garkuwa da mutane kudin fansa.

Majalisar ta amince da hakan ne bayan kyakkyawan dubin da kwamitin harkokin doka yayi kan lamarin, inda ya amince da gyaran fuskar.

Shugaban kwamitin, Sanata Opeyemi Bamidele ne ya gabatar da rahoton. A jawabinsa, ya bayyana cewa babbar manufar dokar itace dakatar da garkuwa da mutane don kudi.

“Samar da dokokin don yakin da hanyoyin samun kudin yan ta’adda ko shakka babu zai taimaka wajen rage cinikayyar bayan fagge cikin al’ummarmu.”

Related posts

Leave a Comment