Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ?aramin ministan man fetur Timipre Sylva ya sanar da cewa zuwa mayun shekara mai zuwa, Najeriya za ta cimma burin Kungiyar Kasashen Duniya masu azrikin man fetur OPEC domin fitar da gangar mai miliyan daya da dubu dari takwas.
Wata sanarwa da mai ba ministan shawara kan harkokin ya?a labarai Horatius Egua ya fitar, ministan ya ce Najeriya za ta yi iya kokarinta domin ?ara tsaurara tsaro kan manyan hanyoyin da bututun mai na ?asar suke da kuma toshe duk wani wuri da yake yoyo a bututan.
Karamin ministan man fetur ?in Timipre Sylva ya bayyana cewa tun asali dalilin da ya sa Najeriya ta kasa cimma muradun kungiyar OPEC ba wai saboda ta kasa ha?o ?anyen man fetur ?in bane, amma saboda kamfanonin da ke ha?o man ba su son tura ?anyen man ta bututan ?asar saboda kada su rinka tafka asara.
Ya bayyana cewa da zarar an ?ara tsaurara tsaro an tabbatar bututan suna lafiya ba su huje ba, za a ci gaba da tura man fetur ?in domin cimma muradin OPEC din na samar da ganga miliyan daya da dubu dari takwas a kullum.
Mista Bala Zaka wanda mai shari ne kan makamashi ya ce akwai yiwuwar kalaman da karamin ministan ya yi za su iya zama gaskiya
Haka kuma ya ?ara jaddada cewa kamfanonin da ke ha?ar mai su ma za su samu tagomashi idan aka magance matsalar fasa bututan mai aka tsaurara tsaro.
Ministan ya ?ara jaddada cewa man da ?asar ke samarwa ya ?aru fiye da a baya inda ya ce a halin yanzu ana samar da sama da ganga miliyan ?aya.
Ministan ya bayyana cewa gyaran da ake yi a halin yanzu na matatun man Fatakwal da Warri da kuma shirin da ake yi na gyaran matatar Kaduna da bude matatar dangote da ke shirin fara aiki duk wani tabbaci ne da Najeriya ke da shi na samar da wadataccen mai
