Babban Bankin Kasa Ya Takaita Adadin Kudin Da ‘Yan Najeriya Za Su Cire A Bankuna

Babban bankin Najeriya CBN ya fitar da sababbin dokoki na hada-hadar ku?a?e a bankunan ?asar.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, CBN ya ta?aita yawan ku?ade la?adan da ?an ?asar za su iya cirewa daga asusun ajiyarsu na banki.

Wannan sanarwa na zuwa ne mako biyu bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya ?addamar da sabbin takardun naira da aka sabunta.

Sabbin matakan da CBN ?in ya fitar a ranar Talata sun ha?a da:

  1. Yawan ku?in da mutum ?aya zai iya fitarwa a banki a sati shi ne naira 100,000 yayin da kamfani zai cire naira 500,000 ne kawai a sati.

Idan mutum na son cire ku?in da ya fi wannan adadi yawa to sai an caje shi kashi biyar cikin 100 ga mutum da kashi 10 cikin 100 ga kamfani na yawan kudin da zai cire.

  1. Duk wanda ya je banki cire kudin da suka haura naira 50,000 da caki na banki da wani ya rubuta masa, to ba za a ba shi kudin ba. Yayin da dokar cire ku?in da suka kai naira miliyan 10 ta amfani da caki a tsakanin bankuna daban-daban tana nan a yadda take.
  2. Yawan kudin da mutum zai iya cirewa ta hanyar amfani da na’urar cire kudi ta ATM a sati kuwa shi ne naira 100,000, wato yawan abin da za a cire a ranar naira 20,000 ne kacal.
  3. Takardun kudin naira 200 kawai bankuna za su dinga lodawa a cikin na’urar ATM.
  4. Idan a wajen masu amfani da na’urar POS ne kuwa, naira 20,000 ce yawan kudin da mutum zai iya cirewa.
  5. A yanayin da ake da tsananin bu?ata kuwa da ba zai wuce sau ?aya a wata ba, inda ake bu?atar cire ku?in da yawansu ya fi wanda aka ?ayyade don wani dalili mai ?arfi, to abin da za a bari mutum ya cire ba zai haura naira miliyan biyar ba, idan kuma kamfani ne to ba zai haura naira miliyan 10 ba.

Sannan a hakan ma sai an caji kashi biyar cikin 100 na yawan kudin ga mutum, da kashi 10 cikin 100 ga kamfani na yawan kudin da za a cire.

Related posts

Leave a Comment