Naira 385 Ya Kamata A Ri?a Sayar Da Litar Mai – Gwamnoni

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da kungiyar gwamnonin kasar ta fitar bayan kammala taronta a ranar Laraba da daddare, wanda aka yi shi ta intanet.

Sun yanke hukuncin ne bayan yin duba ga rahoton da wani kwamiti da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i ya jagoranta da ya goyi bayan janye tallafin mai daga gwamnati.

A yayin gabatar da rahoton a wajen taron, Gwamna El-Rufa’i ya bayyana cewa duk wata gwamnati na kashe tsakanin naira biliyan 70 zuwa biliyan 210 kan tallafin man fetur, wanda ake sayar da litarsa a yanzu kan naira 162.

Ya kuma kara da cewa karin farashin man zai sa a rage fasa kwaurin dangogin man fetur zuwa makwabtan kasashe daga Najeriya, sannan kuma kwamitin rabon arzikin kasa na gwamnatin tarayya FAAC, zai samu tsakanin tiriliyan 1.3 da tiriliyan 2.2 duk shekara.

Kazalika kwamitin gwamnan ya bayar da shawarar cewa gwamnatin tarayya ta sayar da matatun man kasar uku bayan an gyara su.

Sai dai akwai wasu gwamnoni da suka soki shawarwarin da cewa hakan sai kara jefa ‘yan kasar cikin mawuyacin hali, kuma zai yi wahala kungiyar kwadago da ‘yan kasar su yarda.

Sai dai mafi yawan gwamnpnin kuma na ganin gara a janye tallafin man fetur din tun yanzu maimakon a yi ta bata lokaci bayan kuwa an san cewa hakan na da matukar muhimmanci.

Kwamitin ya bayyana jihohin Legas da Oyo da Ogun da Rivers da kuma Abuja a matsayin wadanda suka fi amfani da man fetur.

Ba wannan ne karon farko da aka fara yunkurin janye tallafin man fetur ba a Najeriya. Sai dai a duk lokutan da batun ya taso kungiyoyin kwadago da kuma al’ummar kasar na bujire wa hakan.

Wannan layi ne

Sauran batutuwan da gwamnonin suka cimma

Wannan shi ne karo na bakwai da gwamnonin kasar suka gudanar da taronsu a bana, inda suka tattauna kan batutuwa da dama, kamar yadda AbdulRazaq Bello Barkindo, shugaban tafiyar da harkokin yada labarai da sadarwa na kungiyar gwamnonin Najeriya, ya shaida wa BBC.

Batutuwan da suka tattauna sun hada da:

1. Batun yajin aikin da ma’aikatan shari’a na kasar ke yi, kan neman a ba su damar cin gashin kansu ta fuskar kason kudadensu daga asusun tarayya.

A yanzu dai gwamnonin sun amince da bukatun ma’aikatan shari’ar, amma sun ce sai ma’aikatan sun koma bakin aiki, don a yi tsarin da ya kamata kan lamarin.

2. Kididdigar manoma a Najeriya baki daya, don a san kowane manomi a ina yake da gona, wane irin albarkatun gona yake sarrafawa.

Related posts

Leave a Comment