Na Warke Sarai Daga Ciwo – Tinubu

Jagoran jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, Asiwaju Bola Tinubu, ya koma ?asar bayan ya shafe wata kusan hu?u a birnin Landan sakamakon jinya.

Cikin wata sanarwa daga ofishin ya?a labaransa a ranar Juma’a, Tinubu ya ce ya warke sarai tare da musanta “jitar-jitar da ake ya?awa” kan rashin lafiyar tasa.

Ta ?ara da cewa an yi masa tiyata ne a gwiwarsa ta dama da kuma ba shi kulawar bayan tiyata.

“Mai girma Asiwaju Bola Tinubu ya sauka ne ranar Juma’a 8 ga watan Oktoba da yamma daga Landan,” a cewar sanarwar.

“Sa?anin abin da ake ya?awa, ba a yi masa wata tiyata ba sa?anin wannan sannan kuma babu shirin yi masa wata nan gaba. Ya warke a kan lokaci kuma ba tare da wata matsala ba.”

Cikin sanarwar, Tinubu ya gode wa Shugaba Muhammadu Buhari “saboda ziyartarsa da ya yi a Landan” da gwamnoni da ‘yan majalisar yankin Arewa da ‘yan majalisar Jihar Legas.

An sha ala?anta Bola Tinubu da neman takarar shugaban ?asa a Najeriya, sai dai har yanzu dattijon mai shekara 69 kuma tsohon gwamnan Legas bai bayyana sha’awarsa ba ?arara.

Related posts

Leave a Comment