Na Koma Amfani Da ‘Yata Ne Saboda Tsufan Matata – Mr Akpan

?an sanda sun kama wani mutum mai shekaru 49 a jihar Ogun bayan da ?arsa ta kai rahoton cewa yana yin lalata da ita tsawon shekaru biyar.

Yarinyar mai shekaru 12 ta fa?awa ?an sandan cewa mahaifinta ya fara kwana da ita tun tana ?ar shekara bakwai.

?an sanda sun ce Ubong Williams Akpan ya yi ikirarin cewa matar sa ta tsufa kuma ba ta iya biya masa bu?atar sa, saboda haka ya koma kwanciya tare da ?arsa a madadinta.

Jami’an tsaro sun cafke shi a ranar 2 ga Maris lokacin da yarinyar ta kai rahoton lamarin ga babban jami’in ?an sanda na shiyyar a hedkwatar reshen Itele Ota, Monday Unoegbe, wani babban Sufeton ?an sanda (CSP).

Ta fa?awa ?an sanda cewa mahaifinta ya ci gaba da amfani da ita har tsawon shekaru biyar har sai da ta kasa jurewa kuma dole ne ta kai ?ara ga ?an sanda.

Kwamishinan ?an sandan jihar Edward Ajogun ya ba da umarnin a tura ?arar zuwa sashen tallafa wa iyali na rundunar Ota don cigaba da bincike da kuma gurfanar da shi.

Related posts

Leave a Comment