Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ‘yan Najeriya mazauna birnin tarayya Abuja sun shiga cikin mawuyacin hali sakamakon tsawaitar rashin wutar lantarki.
Sama da wata guda kenan yanzu farashin man Dizel ya yi tashin gwauron zabo lamarin da ya tursasa tsananin wahala da tsadar kayayyakin abinci da mummunan layin mai a gidajen mai.
Rahotanni sun bayyana cewar litar farashin man Dizel ya haura naira 500 lamarin da ya jefa gagarumar matsala ga harkokin kasuwanci da durkushewar gidajen ya?a labarai Talabijin da Rediyo a birnin.
Bincike ya nuna ana sayar da litar man Dizel akan farashin naira 540 zuwa 560 yayin da wasu gidajen man suka dakatar da sayar da Dizel saboda tsadar shi.
Akasarin harkokin kasuwanci a birnin sun tsaya cak biyo bayan matsalar da ake ciki, ko kuma abin da suka mallaka na man ba zai isa gudanar da harkokin su ba.
A halin da ake ciki akasarin gidajen talabijin da rediyo sun shiga matsala biyo bayan wannan kalubale da ake ciki adadin man da suke zuba wa a injinan ba sa isa lamarin da ke haifar musu da rashin cigaba da asara.
A zantawar da aka yi da wasu masu ruwa da tsaki sun yi kira da babbar murya ga gwamnatin tarayya da ta yi gaggawar shigo wa cikin lamarin domin ceto kasar daga barazanar da take ciki.
