Mun Yi Nasarar Hallaka ‘Yan Bindiga 100 A Zamfara – Rundunar Soji

Rundunar sojan Najeriya ta ce dakarunta da ke yaki da ‘yan ta’adda sun yi nasarar kashe ‘yan ta’adda fiye da 100 a arewacin ?asar.

Rundunar ta bayyana haka ne ta bakin kakakinta Benard Onyeuko a ranar Alhamis yayin wani taron manema labarai, yana mai cewa sun cimma nasarar ce cikin mako biyu da suka gabata.

Sojojin sun yi nasarar kashe ‘yan fashin daji 90 tare da ?wato shanu 574 da babur 22 da kuma bindigogi ?irar AK-47 uku a Jihar Zamfara.

Related posts

Leave a Comment