Mun Ceto Dukkanin Daliban Kuriga 137 Daga Hannun ‘Yan Bindiga A Dajin Zamfara – Soji

IMG 20240308 WA0095

Shalkwatar tsaron Najeriya ta ce ta ku?utar da ?alibai 137 na makarantar gwamnati ta Kuriga a ?aramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Darektan da ke kula da harkokin ya?a labarai na tsaron ?asar, Manjo Janar Edward Buba a cikin wata sanarwa, ya ce sun ceto ?aliban su 137 a dajin Zamfara.

A cewar sanarwar, sojojin sun ceto ?alibai mata 76 da kuma maza su 61.

Tun a ranar 7 ga watan Maris ne aka sace ?aliban firamare da na sakandare a makarantarsu da ke ?auyen Kuriga a Kaduna kuma wani malamin makarantar da ya sha da ?yar ya ce ?alibai kusan 287 aka sace.

Malamin makarantar mai suna Sani Abdullahi ya ce an sace ?alibai na ?angaren sakandare 187, sai kuma bangaren firamare ?alibai 100.

“Sojoji tare da jami’an ?aramar hukuma da na cibiyoyin gwamnati sun ha?a hannu wajen ceto ?aliban da aka sace a makarantarsu da ke Kuriga,” in ji Edward Buba.

Sai dai mai magana da yawun shugaban Najeriya, Abdulazeez Abdulazeez ya shaidawa BBC Hausa cewa “?aya daga cikin malaman da aka sace tare da ?aliban ya rasu”.

Tun da farko ?anbindigar sun bu?aci a basu naira biliyan ?aya a matsayin ku?in fansa kafin ranar 27 ga watan Maris domin su saki ?aliban. Kuma babu tabbas ko an biya ku?in fansa kafin ku?utar da ?aliban.

Related posts

Leave a Comment