Babu Wata Gudummuwa Da Gumi Ya Bayar Wajen Ceto Daliban Kuriga – Gwamnatin Kaduna

IMG 20240315 WA0034~2

Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya yi magana bayan kubutar daliban makarantar firamare a jihar. Sani ya ce babu wata rawa da Sheikh Ahmed Gumi ya taka wurin tabbatar da dawowar daliban cikin koshin lafiya.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a yammacin ranar Lahadi 24 ga watan Maris.

Ya ce duk da malamin ya so ya jagoranci sulhu domin kubutar da yaran amma babu wata gudunmawarsa a ciki. Ya kara da cewa yaran 137 da aka sace a ranar 7 ga watan Maris an kubutar da su ne ta taimakon jami’an tsaro a jihar Zamfara.

Har ila yau, gwamnan ya karyata jita-jitar da ake cewa an biya kudin fansa domin ceto yaran daga hannun ‘yan bindiga. “Duk abin da kuke ji shaci-fadi ce kawai na mutane.

Sai dai gwamnan ya bayyana takaicinsa yayin da daya daga cikin malaman da aka sace daliban tare da shi ya rasu. Uba Sani daga bisani ya tura sakon jaje ga iyalan marigayin tare da jajantawa iyalan daliban makarantar.

Related posts

Leave a Comment