Mulkin Najeriya: Tinubu Ya Hau Kura Ba Takunkumi – Atiku

IMG 20240224 WA0211

Tsohon Mataimakin Shugaban ?asa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa salon ?irka gadangar?amar satar ma?udan ku?a?e ne kawai da har Ministan Sufuri, Dave Umahi ya bayyana cewa titin jirgin ?asa da ake ginawa daga Legas zuwa Kalaba, zai lashe Naira tiriliyan 15.6.

Atiku wanda ya yi takarar shugabancin Najeriya a za?en 2023, ya ce Naira tiriliyan 15.6 fa ba ?aramin ku?i ba ne, domin sun kai adadin kasafin ku?a?en jihohin Najeriya 36 baki ?ayan su.

A ranar Alhamis ce dai Minista Umahi ya gana da wasu gidajen talabijin, inda ya bayyana cewa aikin titin jirgin ?asa ?in daga Legas zuwa Kalaba, mai tsawon kilomita 700, zai lashe Naira tiriliyan 15.6. Wato kwatankwacin Dala biliyan 13, kan kowace Dala 1 a Naira 1,200.

Bai da?e da yin bayanin ba sai Atiku ya maida masa kakkausan raddi, inda ya bayyana cewa an dai bu?e wata kafa ce inda za a ri?a ginar ku?a?e ana lodi, ana jida ana gudu da su a ?oye kawai.

Sannan kuma ya ce an bada aikin kwangilar gina titin jirgin ?asa ?in ga kamfanin Gilbert Chagoury, wato Hitech ba tare da bin ?a’idar gayyatar wasu kamfanoni su zo su kawo tandar neman aikin, kamar yadda doka ta tanadar ba.

“Kasafin jihohin Najeriya 36 na 2024 ma fa Naira tiriliyan 14 ne. Idan ka ha?a da na FCT Abuja, kasafin zai tashi Naira tiriliyan 15.91. Amma kuma saboda ganganci da toshewar tunani, za a gina titin jirgin ?asa na Naira tiriliyan 15.6, mai nisan kilomita 700.

“Cikin Satumba, 2023, Umahi ya ce Hitech na Gilbert Chagoury zai gina titin. Sai bayan Girbert ya kammala kar?ar ku?a?en sa a zirga-zirgar jiragen sannan zai dam?a shi a hannun Gwamnatin Tarayya.

“Duk duniya haka kafafen ya?a labarai su ka buga Umahi ya ce a wancan lokacin, har ma da kafafen ya?a labarai mallakar Tinubu.

“To don me kuma yanzu Umahi zai zo ya yi mana ?arya wai Gwamnatin Tarayya za ta bada kaso 15 bisa 100 zuwa 30 bisa 100?”

Atiku kuma ya cika da mamakin yadda ya ce “a cikin kasafin ku?in 2024 aka lissafa aikin titin jirgin ?asa na Legas zuwa Fatakwal kan Naira biliyan 500, kamar yadda Majalisa ta amince, amma kuma sai Gwamnatin Tinubu ta fitar da Naira tiriliyan 1.06 kan aikin. Wato an ru?anya ku?in kenan har da ?oriya. To hakan ke faruwa saboda Majalisar ?asa ba su aikin da ya wajaba su ri?a yi.” Inji Atiku.

Related posts

Leave a Comment