Mataimakin shugaban jam段yyar APC na kasa yankin (Arewa maso Yamma) Salihu Mohammed Lukman, ya yi murabus.
Lukman, a wata wasika mai dauke da kwanan wata 26 ga watan Yuli wacce ya aike wa mukaddashin shugaban jam段yyar na kasa, Sanata Abubakar Kyari, ya ce ya yi murabus ne sabida tsarin da jam段yyar ke shirin dauka ya saba da manufar kafa jam段yyar.
Ya ce, zai zama kunar bakin wake ne a maye gurbin Sanata Abdullahi Adamu, tsohon shugaban jam段yya mai mulki ta kasa da tsohon gwamna Kano, Abdullahi Ganduje.
