Mataimakin shugaban jamiyyar APC na kasa yankin (Arewa maso Yamma) Salihu Mohammed Lukman, ya yi murabus.
Lukman, a wata wasika mai dauke da kwanan wata 26 ga watan Yuli wacce ya aike wa mukaddashin shugaban jamiyyar na kasa, Sanata Abubakar Kyari, ya ce ya yi murabus ne sabida tsarin da jamiyyar ke shirin dauka ya saba da manufar kafa jamiyyar.
Ya ce, zai zama kunar bakin wake ne a maye gurbin Sanata Abdullahi Adamu, tsohon shugaban jamiyya mai mulki ta kasa da tsohon gwamna Kano, Abdullahi Ganduje.

