Rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar Farfesa Umara Babagana Zulum, Gwamnan jihar ya ce mayakan ta’addanci ISWAP sun fi na Boko Haram miyagun makamai, don haka dole a dakile su da gaggawa.
Gwamnan ya yi jawabin ne yayin da ya tarbi mambobin kwamitin majalisar dattawa na kula da harkokin sojoji karkashin jagorancin Ali Ndume.
Shugabannin kwamitin sun ziyarci Gwamna Zulum a Maiduguri, babban birnin jihar domin duba irin cigaban da aka samu a fannin samar da tsaro.
Zulum Yayi jinjina ga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da hukumomin tsaro na tarin nasarorin da suka samu a Borno, Zulum ya bayyana tsananin damuwarsa da karuwar yawan mayakan ISWAP a sassan jihar, musamman a kudancin Borno.
“Zaman lafiya ya fara dawowa a jihar Borno a sannu-sannu. Duk da hakan ba abu mai yuwuwa bane ba tare da agajin gwamnatin tarayya ba.”
Ya kara da cewa: “Shugabannin rundunonin tsaro suna bamu hadin kai yadda ya dace. Tabbas, kwamandan runduna na yanzu da GOCs suna bamu hadin kai. “Hakikanin gaskiya, ya kamata muyi wani abu akan ayyukan mayakan ISWAP a jihar Borno. Idan ba a yi wani abu ba dan ganin an kawar dasu daga jihar, akwai yuwuwar ba mutanen arewa maso gabas kawai ba, gaba daya kasar zamu dandana kudarmu.
A tsokacin da yayi, Ndume ya ce sun ziyarci Borno ne don jinjinawa Zulum game da karfafa sojoji da yake don dawo da zaman lafiya. “Mun zo dubiya ne, gami da mika godiyar mu ga yallabai akan karfafa sojoji da ya ke, wanda su kansu sun yaba,” a cewar Ndume.
