Wasu ?an bindiga da ba a san ko su wanene ba sun ?auke mahaifiyar ?an majalisar Kano, mai wakiltar Maza?ar ?aramar Hukumar Gezawa, Alhaji Isyaku Ali ?anja.
Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa lamarin ya faru ne da misalin ?arfe 1 na dare a jiya Talata a garin Gezawa, inda su ka karya kofar gidan su ka yi awon-gaba da ita.
Da ya ke bada bayanin yadda lamarin ya faru, ?anja ya ce ?an bindigar sun nemi mahaifiyar ta sa da ta bu?e musu kofa amma sai ta ?i bu?ewa.
Ya ?ara da cewa da ta ?i bu?ewa, sai su ka karya ?ofar su ka tafi da ita.
?an majalisar ya ?ara da cewa bayan ?an ta’addan sun bar gidan, sai ?aya da ga cikin samarin da ke kula da mahaifiyar ta sa yai maza ya kira wani abokin siyasar ?an majalisan yansahida masa.
“Tun kafin ma na je Gezawan, tuni Shugaban Caji-ofis na Gezawa ya kira ni a waya, ya shaida mini cewa tuni ma ya aike da jami’an sa zuwa wajen
“Ya gaya min cewa tuni ma sun fara bincike a kan lamarin.
“Sai dai kuma har yanzu maharan ba su tuntu?e mu a kan ta ba. Mu na dai ta yin addu’a kan Allah Ya ku?utar da ita lafiya,” in ji shi.
