Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Mahmud Yakubu, ya bayyana damuwarsa kan ?aruwar matsalar tsaro yayin da zaben 2023 ke ?aratowa.
Yakubu ya yi wannan furuci ne a wurin taron kwamitin tsaro na ha?in guiwa (ICCES), wanda ya gudana a hedkwatar hukumar INEC dake Abuja ranar Juma’a.
Shugaban INEC ya kuma yaba wa hukumomin tsaro bisa namijin kokarin da suka yi wajen tabbatar da tsaro yayin zaben gwamnan jihar Anambra. Sai dai yace yawaitar matsalar tsaro a sassan Najeriya, wata barazana ce kuma abin damuwa game da za?en 2023.
“Game da zaben ?arewar wa’adi, muna da manyan za?ukan dake tafe cikin wannan shekarar 2022. Za?en gwamnan jihar Ekiti zai gudana ranar 18 ga watan Yuni, 2022 da kuma na jihar Osun ranar 16 ga Yuli, 2022.” “Sannan akwai zaben kananan hukumomi na Abuja da za’a gudanar nan gaba ka?an.
