Kano: Za Mu Tabbatar Doka Ta Yi Aiki Akan Makasan Hanifa – Ganduje

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar Gwamnan jihar Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayar da tabbacin cewa gwamnati za ta ci gaba da sanya ido sosai tare da tabbatar da hukunta duk wanda aka samu da laifi a yin garkuwa da kisan gilla da aka yi wa Hanifa Abubakar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labaran jihar Malam Muhammad Garba ya fitar.

Gwamnan ya ce tuni matakan da aka dauka a lamarin sun fara aiki, ciki har da rufewa da kuma janye lasisin gudanar da makarantar ba tare da bata lokaci ba.

Related posts

Leave a Comment