Matsalar Tsaro Zai Durkusar Da Najeriya – Sarkin Musulmi

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar mai alfarma Sarkin musulmi Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III ya bayyana yadda matsalolin tsaro suka zama babbar matsala ga Najeriya.

Ya bayyana haka ne a wani taron tattaunawa ta musamman da jaridar Daily Trust ta safiyar ranar Alhamis. Alhaji Sa’ad, ya kuma bayyana abubuwan da ake bukata daga shugabannin kasar nan, inda yace ba zai yiwu kasar ta ci gaba ba a hannun shugabanni masu son kai.

“Idan babu tsaro, ba za mu ci gaba ba.” Da yake magana kan abin da ya kamata a mayar da hankali a kai, ya bayyana cewa: “Na fi damuwa da rashin tsaro domin shi ne babban shinge ga kowane bangaren tattalin arziki a duniya.”

Idan babu tsaro bautar Allah ma ba za ta yiwu ba Hakazalika, ya kuma jaddada dogewarsa kan yiwa kasar fatan alheri da tuni ga shugabanni kan abin da ke kansu na ciyar da kasa gaba, inda yake cewa: “Ba za mu iya gajiya ba kuma kada mu gaji da maganar zaman lafiya.

Ya kuma yi bayanin cewa, shugabanni masu son kai ba za su kai kasar ga tudun mun tsira ba, don haka akwai bukatar a jawo hankalin shugabanni su zama masu kyautatawa mabiyansu. “Ba za ka iya zama shugaba ba idan kana da son kai. A ko da yaushe za mu ke jawo hankalin shuwagabannin mu wajen kyautatawa.”

Related posts

Leave a Comment