Rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar Gwamnan Jihar Farfesa Babagana Umara Zulum ya dawo gida Najeriya bayan shafe hutun makwanni uku da ya yi yana aikin Umrah a kasar Saudiyya.
Gwamnan ya samu tarba daga manyan mukarraban gwamnatin jihar ?ar?ashin Jagorancin mataimakin Gwamnan Jihar wanda ya rike ragamar mulkin Jihar a tsawon makwanni da gwamnan ya ?auka baya Jihar.
Hakazalika dimbin jama’a mazauna birnin na Maiduguri sun fito kwai da kwarkwarta wajen tarbar Gwamnan da nuna karsashi da farin ciki na dawowarsa lafiya.
A jawabin da ya gabatar Gwamna Zulum ya godewa jama’ar Jihar ta Borno bisa ga goyon bayan da suke ba Gwamnatin shi inda ya sha alwashin yin dukkanin mai yiwuwa wajen ganin Jihar ta cigaba.
