Matsalar Tsaro: Yau Alhamis Ne Aka Shirya Buhari Zai Gurfana Gaban Majalisa

Ana tsammanin Shugaban kasar zai amsa kirar Majalisar ne a ranar yau Alhamis 10/12/12, domin ?arin haske akan halin da tsaron ?asar ke ciki, da matakan da gwamnati ke ?auka na magance matsalar.

Amma a halin yanzu babu tabbas hakan zai faru biyo bayan kalaman da Ministan Shari’a Abubakar Malami ya yi da cewar a ?ar?ashin doka majalisa bata da ikon tilasta wa shugaba Muhammadu Buhari ya gurfana gabanta domin bayani akan halin da tsaron ?asa ke ciki.

Inda jama’a basu manta ba a makon da ya gabata ne majalisar wakilai ta tarayya ta cimma matsayar gayyatar shugaban ?asar don yi mata bayani kan ta?arbarewar tsaro a ?asar a wani zama da tayi karkashin jagoracin kakakin majalisa Femi Gbajabiamila.

Majalisar ta dauki wannan matakin ne bayan halaka manoma 43 da ‘yan ta’addan Boko Haram suka yi a garin Zabarmari dake yankin ?aramar Hukumar Jere ta jihar Borno ta hanyar yankan Rago.

An shirya cewa shugaban zai gurfana gaban majalisar a yau Alhamis amma yanzu babu tabbacin zai amsa kirar.
A cikin sanarwar da ya fitar a ranar Laraba, Malami ya ce, “majalisar tarayya bata da iko ko karfin neman shugaban kasa ya gurfana gabanta a kan ayyukan dakarun sojoji”.

Majalisar ta aike wa shugaba Muhammadu Buhari gayyatar ne don karin hare hare da ake samu na ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda a kasar musanman yankin Arewacin Kasar.

Related posts

Leave a Comment