Rahoton dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar tsohon shugaban hukumar za?e mai zaman kanta, INEC, Farfesa Attahiru Jega, ya yi garga?in cewa matukar ba’a shawo kan matsalar tsaro ba, babban zaben 2023 ba zai yiwu ba.
Farfesa Jega ya yi wannan furucin ne ranar Alhamis a Ibadan, yayin da yake jawabi na musamman a wurin bikin cikar tsohon gwamnan Oyo, Abiola Ajimobi, shekara 72, wanda ya gudana a jami’ar Ibadan.
Jega ya ?ara jaddada cewa tsaro babban jigo ne na kowane irin za?e, matukar ana son kowace jam’iyya ta amince da sakamakon wannan zaben.
A cewarsa, matsalar tsaro dake ?ara mamaye ?asar nan wani babban barazana ce ga shirin gudanar da za?en 2023. Jega wanda kwararre ne a ilimin kimiyyar siyasa, yace wajibe ne a magance duk wani ?alubalen tsaro domin tabbatar da za?e mai zuwa.
“Har sai an gudanar da za?e a wuri mai zaman lafiya da kwanciyar hankali, idan ba haka ba gaskiya da kuma sahihancin sakamakon za?en zai zama abin tantama.”
“Shi kalubalen tsaro yana rushe ingancin za?e ne baki ?aya. Kuma yana lalata duk wani shiri na gudanar da za?en ya hana yin za?en. “Matsalar tsaro zata sanya babu wanda zai kalli sakamakon za?en da mutunci balle ya amince da shi.” Daga nan kuma, Jega ya kara da garga?in cewa yayin da zaben ke kara kusantowa ne ?alubalen tsaro ke ?ara yawaita, kuma hakan babbar barzana ce.
