Matsalar Tsaro A Makarantu: Amfani Da CCTV Zai Taimaka – Sani

Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani, ya ba jami’an tsaro hanyoyin kulawa da makarantu a arewacin Najeriya, inda ya bukaci yin amfani da na’urorin kamara na CCTV a matsayin wata hanya mafita akai.

Tsohon Sanatan ya bayar da shawarwarin ne a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter a ranar Asabar, bayan sace daruruwan daliban GSSS Kankara a jihar Katsina da wasu ‘yan Bindiga suka yi.

Sanata Shehu Sani, wanda ya wakilci mazabar Kaduna ta tsakiya, yayi kira akan rufe duk makarantun kwana dake kauyuka.

Ya kuma bayar da shawara, inda yace ya kamata a hora dalibai da malaman makarantu don su san yadda za su yi idan wani rikici ko tashin hankali ya same su, cikin gaggawa. Ya ce, ya kamata a sanya na’urar daukar hotuna ta CCTV, kuma su samar da hanyoyin sanar da matsalaloli cikin gaggawa a makarantun.

Shehu Sani ya nuna alhininsa a kan wadanda suke alfahari da samun nasarar ceto yaran, bayan babu wanda ya amince da cewa laifinsa ne rashin ceton manoman Zabarmari na jihar Borno da ‘yan Boko Haram suka yi.

A cewarsa, ya kamata a ce shugabanni sun cire batun jam’iyya ko kuma ra’ayin siyasa, su yi kokarin taimakon kasar nan.

Related posts

Leave a Comment