Babban Sakataren ?ungiyar Izala na ?asa Sheikh Kabiru Haruna Gombe ya bayyana cewar matsalar tsaro dake addaba Najeriya musamman yankin arewacin ?asar a yanzu, matsala ce da ta gagari shugaban ?asa da sauran masu rike da madafun iko a kasar.
Sheikh Gombe ya bayyana hakan ne a yayin bu?e karatun tafsirin Alqur’ani mai girma da ya gabatar a masallacin ?ungiyar Izala dake birnin tarayya Abuja.
Babban malamin ya kara da cewar a halin da ake ciki yanzu babu inda tsaro yake a kasar, ‘yan ta’adda da sauran miyagu na cin karensu babu babbaka a har kullum.
“A halin da ake ciki yanzu da akwai bayin Allah masu maras adadi da’yan Bindiga suka sace suna azabtar dasu a dokar daji babu ci babu sha, an yi wa Mata masu yawa fyade an kashe jama’a da dama wadanda ba su san hawa ba ba su san sauka ba! Allah mun tuba”.
“Tabbas Buhari ya gaza, gwamnoni sun gaza, Ministoci da sauran ‘yan majalisu sun gaza, sojoji da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro sun gaza, kowa ya gaza babu abin da ya saura sai mu koma ga Allah!”
