Masarautar Daura Ta Nada Uwargidan Okorocha Sarautar Zinariyar Hausa

Rahotanni daga Masarautar Daura dake jihar Katsina na bayyana cewar mai Martaba Sarkin Daura Alhaji Umar Faruoq Umar ya na?a uwargidan tsohon Gwamnan Jihar Imo Rochas Okorocha Sarautar Zinariyar Kasar Hausa.

Na?in nata ya biyo bayan irin gudummawar da Masarautar tace take bayarwa wajen inganta rayuwar al’ummar Hausawa a yankin Kudancin Najeriya.

Tun da farko sai da Masarautar ta yi nadi ga Rochas Okorocha Sarautar Maga Alherin Kasar Hausa, bisa jajircewarshi akan ciyar da yankin Arewa.

Masarautar Daura dai ita ce uwar Masarautun Kasar Hausa, wadda masana tarihi suka tabbatar ta kafu tun shekaru 2000 da suka gabata.

Related posts

Leave a Comment