Jam iyar P D P a jahar Adamawa ta zabi sabbin shuwagabanin ta wadanda zasu jagoranci harkokin jam iyar nan da shekaru hudu masu zuwa.
Da yake jawabi jin kadan da kammala zaben shugaban kwamitin zaben kana gwamnan jahar Bayelsa Dauye Diri ya yaba da yadda aka gudanar da zaben wanda zaben ya gudana ne bisa tsarin jam iyar ta P D P.
Ya kuma godewa tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar bisa goyon baya da hadin kai da ya bayar wajen gudanar da zaben shuwagabanin jam iyar dake jahar Adamawa.
Shima anashi jawabi sabon zababben shugaban jam iyar P D P a jahar Adamawa Barista A T Shehu baina farin cikinsa yayi dangane da nasara da ya samu tare da godewa yayan jam iyar bisa hadin kai da goyon baya da suke baahi.
A T Shehu ya kuma tabbatar da cewa zaiyi aiki kafada da kafada da membobin jam iyar domin ganin an samu cigaba da kuma samun nasara a zaben shekara ta dubu biyu da ashirin da uku.
Baya ga tsahon matai making shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar taron ya samu halartan tsahon gwamnan jahar Adamawa Mr Boni Haruna da dai sauransu.
