Majalisa Ta Yi Kiran A Gaggauta Sallamar Shugaban Hukumar Kwastam

Rahotanni daga babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Majalisar tarayya ta nemi a sauke shugaban hukumar Kwastam, Hamid Ali nan take ba tare da ?ata lokaci ba.

Shugaban kwamitin dake kula da ayyukan hukumar a majalisar, Francis Fadahusin wanda tsohon kwatirola ne a hukumar ya bayyana haka.

Yace, idan dai gwamnatin tarayya zata iya sauke shugabar NPA, Hadiza Bala Usman, to ya kamata shima shugaban Kwastam, Hamid Ali a saukeshi.

Yace saboda ana tafka gagarumar rashawa da cin hanci a karkashinsa. Kuma hakan yana sanya Najeriya na tafka asarar kudin shuga da yawa.

Yace kudin kayan da ake kwacewa da wanda hukumar ke sayarwa basa shiga cikin Asusun gwamnati, dan haka indai Gwamnatin da gaske take game da yaki da rashawa da cin hanci to ta sauke Hamid Ali.

Related posts

Leave a Comment