Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar rundunar ‘yan sanda ta ?asa ta sayo sabbin jiragen ya?i marasa matu?a har guda biyar da zimmar kawar da ta’addanci.
?aukar matakin rundunar ‘yan sandan ya biyo bayan yadda ayyukan ta’addanci ke karuwa ‘yan kwanakin nan musamman a arewacin kasar.
Harin da ‘yan bindiga suka kai kan jirgin Abuja-Kaduna ranar Litinin ya haifar da cece kuce a fa?in ?asar.
Tuni shugaban kasa ya bada umarnin ga jami’an tsaro su yi dukkannin mai yiwuwa wajen magance matsalar wadda ke neman gagarar kundila.
