Kano: Hukumar Yaki Da Rashawa Ta Yi Sammacin Ganduje


Hukumar kar?ar ?orafe-?orafe da hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta ce ta aika takardar gayyata ga tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje a kan ‘bidiyon dala’.

Wata sanarwa da hukumar mai taken (KPCACC) ta fitar, na cewa ta gayyaci Ganduje ne domin ya je ya wanke sunansa game da binciken da ake yi.

A shekarar 2017 ne, jaridar Daily Nigerian da ake wallafawa a intanet, ta fitar da jerin bidiyon da ke nuna wani mutum wanda ta yi zargin cewa Ganduje ne yake kar?ar damin daloli daga hannun wasu ‘yan kwangila yana zubawa a aljihu.

Sanarwar ta ambato shugaban hukumar ?orafe-?orafe, Muhyi Magaji Rimin Gado yana cewa: “Na sa hannu a kan wata wasi?a don gayyatar shi, ya zo a yi masa tambayoyi a hukumar cikin makon gobe. Saboda abin da doka ta ce kenan kuma za mu bayar da ?umbin damammaki don ya kare kansa”.

Sai dai, Mallam Muhammad Garba, tsohon kwamishinan ya?a labarai na Kano kuma makusancin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ce har yanzu ba su samu takardar gayyatar da ake cewa hukumar ta aika wa tsohon gwamnan ba.

Kuma dangane da sahihancin bidiyon da hukumar Muhyi take i?irari, Muhd Garba ya ce ba za su ce uffan a kan wannan batu ba, don kuwa magana ce da take gaban kotu.

Umar Abdullahi Ganduje dai ya sha musanta zargin, inda ya ri?a i?irarin cewa abokan adawa ne suka shirya ma?ar?ashiya da nufin hana masa damar shiga za?en 2019.

Lamarin dai ya janyo matu?ar ce-ce-ku-ce, ba kawai a Kano ba har ma da Najeriya gaba ?aya, abin da ya kai har majalisar dokokin jihar kafa kwamiti domin binciko gaskiyar lamarin.

Sanarwar dai ta ce hukumar kar?ar ?orafe-?orafe ta Kano ?ar?ashin jagorancin Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado ta nuna aniyar yin bincike tun sa’ar da bidiyon ya bayyana, sai dai a lokacin Ganduje yana da rigar kariya a matsayinsa na gwamna.

Gwamnatin Ganduje a watan Yulin 2021, ta dakatar da Muhyi Magaji daga shugabancin hukumar kar?ar ?orafe-?orafe da hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano, lamarin da ya janyo ta?addama, har Muhyi ya garzaya kotu.

Gwamnatin a wancan lokaci ta zargi Muhyi Rimin Gado da ?in aiki tare da wani jami’i da ma’aikatar ku?i ta aika hukumar, abin da ya janyo Ganduje ya sallame shi daga aiki a 2022.

Sai dai, shugaban hukumar kar?ar ?orafe-?orafen ya ci gaba da ?alubalantar matakin da gwamnatin Ganduje ta ?auka, kuma ya nemi kotu ta tabbatar masa da ‘yancinsa na ?an’adam.

Daga bisani, kotu ta yanke hukuncin da ya bai wa Muhyi gaskiya, kuma ta ba da umarnin a mayar da shi kan mu?aminsa.

A watan Yunin 2023 ne kuma, sabuwar gwamnatin Kano da Abba Kabir Yusuf ke jagoranta, ta mayar da Barista Muhyi Magaji Rimin Gado kan mu?amin shugaban hukumar ya?i da cin hanci da rashawa ta Kano.

A cikin sanarwar da hukumar ta fitar ranar Alhamis, Muhyi Rimin Gado ya ce bayan ya koma shugabancin a ‘yan makwannin da suka wuce ne, suka yanke shawarar sake bu?e binciken.

Ya ce zuwan Abdullahi Ganduje gaban hukumar don wanke kansa ko akasin haka, abu ne mai fa’ida saboda “bidiyon na ci gaba da janyo wa jihar da ma al’ummar jihar muzantawa a fa?in duniya”.

Related posts

Leave a Comment