Mafusata Sun Bankawa Ofishin INEC Wuta

Rahotanni daga Jihar Abia na bayyana cewar a ranar Lahadi 9 ga wata wasu gungun Matasa ‘yan bindiga sun kutsa kai babban ofishin hukumar zabe mai zaman kanta na kasa INEC dake Umuahia babban birnin Jihar Abia inda suka cinna wuta a ofishin hukumar.

A jawabin kwamishinan ya?a labarai na INEC yace kwanan nan aka gyara ofishin da mutanen suka ?ona. Wannan na ?unshe ne a wata takarda da INEC ta fitar a shafinta na kafar sada zumunta wato Tuwita.

A jawabin dake jikin takardar, INEC tace wannan ba shine karo na farko da aka kaiwa ofishin hukumar hari a jihar ba. Jawabin yace: “Hukumar INEC tayi zama ranar 10 g watan Mayu, ta kuma tattauna akan abubuwa da dama wa?anda suka ha?a da rahoto mara da?i daga jihar Abia.”

“Kwamishin za?en jihar ya kawo rahoton cewa yan bindiga sun sake ?ona ofishin da hukumar ta gyara a baya-bayan nan a ?aramar hukumar Ohafia.”

“Lamarin ya faru ne a daren ranar Lahadi 9 ga watan Mayu, 2021, babu wani rahoton rasa rai ko jin rauni daga ?angaren ma’aikatan mu da kuma masu gadi amma ginin wajen ya ruguje, sannan kuma duk wasu kayayyakin mu dake ciki sun ?one.”

“Amma an mi?a rahoton duk abinda ya faru ga hukumar yan sanda domin su gudanar da Bincike.” Idan baku manta ba a makon da ya gabata INEC ta samu rahoton kai hari a ofishinta dake karamar hukumar Essien Udim a jihar Akwa Ibom.

INEC ta nuna matu?ar damuwarta kan hare-haren da ake kaiwa ofisoshinta wanda hakan ka iya jawo koma baya ga ayyukanta wa?anda suka ha?a da; cigaba da rijistar cancantar ka?a ?uri’a, gyara da kuma ?ara runfunan za?e, Za?en cike gurbi da kuma babban za?en 2023 dake tafe.

Related posts

Leave a Comment