Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya nuna rashin jin da?insa bayan gwamnatin Najeriya ta dakatar da gudanar da jarrabawar kammala sakandare ta WAEC a ?asar.
A wani sa?o da ya wallafa a shafinsa na Twitter, tsohon mataimakin shugaban ?asar ya bayyana cewa akwai hanyoyin da gwamnatin za ta iya bi wurin gudanar da jarrabawar ba wai ta dakatar da ita baki ?aya ba.
Cikin hanyoyin da ya lissafo akwai batun amfani da manyan ?akunan taro na ?asar da makarantun firamare da filayen wasanni da sauran wurare domin amfani da su wurin gudanar da jarrabawar.
Ya bayyana cewa dama tuni sauran ?asashen Afirka suka bar Najeriya a baya a fannin ilimi, ya kuma ce wannan yun?urin na dakatar da jarrabawar zai iya jawo rikici a ?angaren ilimi a ?asar.
Ya yi garga?in cewa idan gwamnatin ?asar ba ta bari an gudanar da jarrabawar ba, dubban mutane za su ?etara ma?wafta domin zana jarrabawar.
